Rahoton ya ci gaba da cewa; Kungiyar leken asirin ta CIA ta tattara bayanai mabanbanta wadanda su ka tabbatar da cewa yarima mai jiran gadon na Saudiyya ne ya bayar da umarnin kashe Jamal Kashoogi.
Bugu da kari kungiyar leken sirin ta Amurka ta saurara ta kuma ji maganganun wayar tarho na Khalid Bin Salman, jakadan Saudiyya a kasar Amurka.
Jaridar ta Washington Post ta kuma bayyana cewa; Khalid Bin Salman ya yi magana ta watar tarho inda ya bukaci Jamal Kashoogi da ya tafi karamin ofishin jakadancin Saudiyyar da yake a Istanbul na kasar Turkiya
Bugu da kari, Kungiyar leken asirin ta Amurka ta saurari faifen sauyi na maganganun da su ka gudana a yayin kashe Kashoogi wanda jami'an leken asirin Turkiya su ka saurara